Mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin sama ya yi hatsari a Kazakhstan

0 43

Gomman mutane sun mutu bayan da wani jirgin sama mai ɗauke da fasinjoji 67 ya yi hatsari a Kazakhstan, kamar yadda rahotanni daga ƙasar suka nuna.

Hukumar agajin gaggawa ta ƙasar ta ce mutane 25 sun tsira daga hatsarin.

Jirgin saman, wanda na kamfanin Azerbaijin ne, ya kama da wuta ne, sannan ya faɗo a kusa da birni Aktau.

Amma har yanzu ba a san dalilin hatsarin jirgin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: