Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da batan wasu 15 a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku jiya a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Dutse.
Mista Shiisu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Nahuce da ke karamar hukumar Taura (LGA) ta jihar.
Ya kara da cewa bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki na cikin gida da Samariyawa nagari, sun yi tururuwa zuwa wurin da lamarin ya faru domin gudanar da aikin ceto.
Ya bayyana sunayen fasinjojin da suka rasu da Abdurra’uf Mohammed mai shekaru 15 da Suleman Ali mai shekaru 20 da Shafiu Mohammed mai shekaru 25 da Ado Nafance mai shekaru 7 da Alasan Mohmmed mai shekaru 16 dukkansu daga karamar hukumar Taura.
A cewarsa, an kara kaimi wajen kwato sauran fasinjoji 15.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa lamarin na zuwa ne wata guda bayan wani abu makamancin haka a kauyen Kwalgai dake karamar hukumar Auyo, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da ceto wasu 18.