Mutane 4 sun rasa rayuwar su a wani mummunan hatsari da ya auku a jihar Bauchi

0 236

Mutane 4 sun rasa rayuwar su a wani mummunan hatsari da ya auku a jihar Bauchi, kamar yadda hakumar kiyaye Aukuwar hadura ta kasa FRSC ta bayyana.

Lamarin ya faru ne a ranar asabat data gabata, a kauyen Rinji dake karamar Toro a wanda ya rutsa da fasinjoji.

Hakumar ta bayyana damuwar ta karuwar hadura da ake samu a baya-bayan nan, saboda haka ne babban kwamandan rundunar na kasa Dauda Ali Biu ya kaddamar da wata tawagar karta kwana domin kamawa da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da aikata laifuka da take dokokin kan hanya dana tuki. A cewar kakakin hakumar tawagar karta kwanan ta hada da jami’ai daga hakumar tsaron farin kaya Sibil defens, da hakumomin kuda da zirga-zirga na jihohi da kuma jami’ansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: