Mutane 4 ne suka mutu a wani hadari daya faru akan hanyar Gumel zuwa Kano

0 531

Akalla mutum 4 ne suka mutu wasu 10 suka samu raunuka wani hadari daya faru tsakanin wasu motoci biyu akan hanyar Gumel zuwa Kano.

Jami’in yada labarai na hukumar kare afkuwar haddura ta kasa Mr Ibrahim Gambo ne ya bayyana hakan a lokacin dayake gabatar da Rahoton mako mako yau a babban birnin jihar Jiogawa Dutse.

Mr Ibrahim Gambo ya fadawa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne a jiya da misalin karfe 12 da mintina 25 a lokacin da motocin biyu sukayi karo da junansu a daidai kauyen Achauya dake karamar hukumar Gumel.

Ya kara da cewa anan take fasinjoji 4 suka mutu bayan likitoci sun tabbatar da mutuwar su, sai kuma wasu Maza 7 da mata 3 da yanzu haka suke karbar magani a asibiti.

Mr Ibrahim Gambo ya kuma bukaci masu ababen hawa da su guji tuki da daddare sannan su kasance masu kiyaye dokokin tuki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: