MURIC ta yi Allah wadai da kisan wani Mahauci da aka yi a Sokoto

0 328

Kungiyar kare hakkin Musulmi  MURIC ta yi Allah wadai da kisan wani Mahauci Usman Buda, da aka yi a Sokoto kan zargin yayi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar shiyyar Sokoto Muhammadu Mansur Aliyu ya fitar, ya bukaci Musulmi da su daina daukar doka a hannun su a duk lokacin da ake zargin wani yayi kalaman batanci ga Annabi.

Muhammad Mansur, Ya bayyana cewa dokar addini Musulunci ta bada umarnin yin hukunci ga wanda yayi batanci ga Annabi SAW, ya kamata a tabbatar da shi ta hanyar shaidu a gaban kotu, kuma kotu ce zata yi  hukunci kan irin wannan laifin kafin hukuma ta zartar da hukuncin kisa.

Shugaban kungiyar kare hakkin Musulmin, Ya kuma yi Allah wadai da kisan Mahaucin,inda ya bukaci Musulmi da su dai na wasa da shari’a, su bari doka ta zartar da hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: