Kungiyar Kwadago ta kasa ta yi gargadin cewa ta gwammace ta tattara ma’aikata su zauna a gida tare da iyalansu ko kuma su ba da hidima kyauta maimakon karbar mafi karancin albashin Naira dubu 48,000 da gwamnatin tarayya zata bayyana a gobe Talata.
Mataimakin shugaban kungiyar ta NLC, Farfesa Theophilus Ndubuaku ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi.
A ranar Laraba ne kungiyoyin NLC da kungiyar TUC suka fice daga tattaunawar bayan da gwamnatin tarayya ta yi tayin biyan Naira dubu 48,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, adadin da ya yi kasa da Naira dubu 615,00 da kungiyoyin suka nema a matsayin sabon mafi karancin albashi a kasar nan.
Bayan zaman, shugabannin ƙwadago sun shaida wa manema labarai a wani taron gaggawa da suka yi cewa, hakan wani cin fuska ne ga haƙƙin ma’aikatan Nijeriya.