Muhimmin bayani kan kamawa makaranta a Jigawa ranar Litinin

0 242

Gwamantin jihar Jigawa ta amince a bude makaratun fririmare da na sakandire a ranar litinin 26 ga watan nan a fadin jiha.

Kwamishinan yada labarai na jihar nan Malam Ibrahim Mamser ne ya bayyana hakan bayan zaman majalissar zartarwa ta jihar da aka gudanar karkasahin gwamna Muhammadu Badaru Abubakar a gidan gwamanti dake dutse.

A tsarin jadawalin komawar, Yan makarantun kwana zasu koma a ranar lahadi 25 ga watan oktoba, sannna bayan kwana daya sauran yan makarantun jeka ka dawo su koma a ranar litinin 26 ga watan nan da muke ciki.

Sannan ya kara da cewa yaran firimare yan aji 1 zuwa 3 za suna zuwa da safe sannan yan aji 4 zuwa aji 6 zasu na zuwa da yamma.

Kazalika ya kara da cewa yan karamar sakandire zasu na zuwa makarantun su da safe, kana daga bisani yan yan babbar sakandire zasu na zuwa da yamma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: