Ministan wutar lantarki ya sha alwashin gwamnatin tarayya zata inganta wutar lantarki
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta samar da wutar lantarki ga al’ummomin da ba su amfani da wutar lantarkin a Najeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin da yake duba aikin tare da tantance tasirin wutar mai karfin kilo watt 90 a Adafila, Ogbomoso, a wani bangare na rangadin aikin da ya ke yi na samar da wutar lantarki a Najeriya.
Adelabu ya ce aikin zai iya samarda wutar lantarki ga gidaje sama da 1,300 da suka hada da dakunan shan magani, makarantu, da kananan ‘yan kasuwa a cikin al’umma. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun da farko ministan ya kai ziyarar dudduba ayukka a tashoshin samar da wutar lantarki mai karfin kilo vat 132 a Oyo da Ogbomoso.