Ministan wutar lantarki ya gana da Tinubu kan matsalar wutar arewacin Najeriya

0 161

Ministan wutar lantarki a Najeriya Adebayo Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakai na laluɓo wasu hanyoyin samar da lantarki ga jihohi da ke arewacin Najeriya.

Adelabu ya ce gwamnatin za ta yi haka ne domin rage wa ƴan yankin raɗaɗin rashin wutar da suke ciki sakamakon lalata layukan bayar da hasken wuta a faɗin yankin.

Ministan na magana ne bayan wata ganawa da ya yi da shugaba Bola Tinubu a yau Litinin, inda ya ce da farko ana sa ran amfani da wata karamar tashar bayar da lantarki ta Ikot Ekpene wadda ta fito daga Calabar domin kai lantarki yankin arewa, sai dai layin ya lalace.

“Muna ci gaba da ƙoƙarin ganin mun gyara layin. Kuma idan kuka tuna a taron majalisar zartaswa da ta gabata, ma’aikatar wutar lantarki ta buƙaci a gyara tare da inganta layin bayar da wuta ta Shiroro, wanda shi ke samar da wuta a faɗin arewa,” in ji ministan.

Adelabu ya ƙara da cewa matsalar ta rashin wuta ta shafi jihohi 17 a faɗin arewacin Najeriya.

“Mun tattauna abin da ya janyo matsalar, wanda hakan ya faru ne sakamakon lalata layukan bayar da wuta na tashar samar da wuta ta Shiroro,” in ji shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: