Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya gabatar da shirinsa kan makomar Gaza
Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya gabatar da shirinsa kan makomar Gaza, bayan kammala yaƙi.
Amurka ta daɗe tana matsa wa gwamnatin Isra’ila lamba da ta bayyana shirinta a fili.
Yoav Galanta ya ce Falasdinawa ne ke rayuwa a Gaza, don haka za su ci gaba da jagorancin yankin, amma bisa sharaɗin cewa babu zaman doya da manja da Isra’ila, kuma babu shirya mata wata kutungwila. A cewarsa, yanzu yaƙin da Isra’ila ke yi a zirin zai fi mayar da hankali kan kudancin yankin, kana za su ci gaba da ƙoƙarin ganin sun kashe shugabannin ƙungiyar Hamas, ko a ina suke a doron duniya.