Ministan Shari’a ya yi alkawarin sake duba dokar da ta haramta yunkurin kunar bakin wake a Najeriya

0 238

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi alkawarin sake duba dokar da ta haramta yunkurin kunar bakin wake a kasar.

Ya yi alkawarin ne a lokacin da ya karbi tawagar gidauniyar Asido, wata kungiya mai zaman kanta da ke inganta harkar kula da lafiyar kwakwalwa da kawo gyara.

Ya ce doka abu ne da ya kamata a sake dubawa, musamman ma inda aka tabbatar cewa masu laifin ba su da hankali. 

Tun da farko, wanda ya kafa Asido, Dokta Jibril Abdulmalik, ya bayyana cewa halin da ake ciki abin da suke bukata shi ne taimako da magani, ba horo da dauri ba. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: