Ministan ma’adanai ya gabatar da sabbin sarrfaffen Zinare da aka tace ga shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa dake Abuja
A wani muhimmin mataki na haɓaka tattalin arzikin Nijeriya, ministan ma’adanai, Dele Alake, ya gabatar da sabbin sarrfaffen Zinare da aka tace ga shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Waɗannan sandunan zinare, sun cika ƙa’idar inganci na kasuwar Bullion ta London, hakan na nuna ma’amalar kasuwanci ta farko a ƙarƙashin shirin kasuwancin Zinare na Ƙasa (NGPP), wanda aka ƙera don ciniki da sayen zinare daga ƙananan ma’aikatan ma’adinai.
Alake ya bayyana irin tasirin da wannan sabon shirin ya yi ga tattalin arziki nan take, inda ya ce tuni ya bayar da gudunmawar sama da Dala miliyan $5m ga asusun ajiyar Najeriya na ƙasashen waje tare da zuba kusan Naira biliyan ₦6b a tattalin arzikin karkara.
Wannan shiri, in ji shi, yana amfani da Naira ta Najeriya wajen siyan gwal, wanda a al’adance ake yin ciniki da dala, ta yadda za a samu kwanciyar hankali a kasafin kuɗi.
Za a sayar da gwal din ne ga babban Bankin Najeriya (CBN), wanda kai tsaye zai haɓaka asusun ajiyar ƙasar waje da kuma iya daidaita darajar Naira. Wannan tsarin na nufin samar da yanayi mai kyau ga masu son zuba jari na ƙasashen waje.