Ministan harkokin wajen Mali ya nemi majalisar dinkin duniya ta yi gaggawar janye dakarunta daga kasarsa
Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop, yayi kira ga majalisar dinkin duniya ta janye dakarunta na wanzar da zaman lafiya daga kasarsa ba tare da bata lokaci ba.
Abdoulaye Diop ya zargi dakarun wanzar da zaman lafiyar da kasancewa bangare na matsalar dake kara rura wutar rikici tsakanin kabilu.
Yana jawabi ne ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.
Dakarun wanzar da zaman lafiyar na da sojoji sama da dubu 13. Kuma aikinsu na shekaru 10 ya gaza kawo karshen hare-haren masu ikirarin jihadi.
Kamfanin tsaro na Wagner na kasar Rasha ne ke taimakawa sojojin dake mulkin Mali.
Jami’an kasashen yamma suna zargin kamfanin Wagner da cin zarafin bil-adama a kasar Ukraine da sassan Afrika.
Kamfanin Wagner bai ce uffan ba dangane da zarge-zargen kasashen yamma kuma ayyukansa a Mali da sauran sassan Afrika ya kasance cikin sirri.