Ministan ayyuka ya kaddamar da babban titin Sokoto – Badagary mai tsawon kilomita 258

0 218

Ministan ayyuka David Umahi ya kaddamar da babban titin Sokoto-Badagary mai tsawon kilomita 258 a jihar Kebbi da kuma mai tsawon kilomita 120 a jihar Kebbi.

Da yake kaddamar da shirin a masaukin shugaban kasa a Birnin Kebbi, ministan ya ce idan aka kammala ayyukan za su bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Umahi ya bayyana cewa, ginin Greenfield zai ba da damar haɗa fasahohin zamani, da rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta tsaro. A nasa jawabin, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan sabunta hanyoyin, inda ya kara da cewa hakan zaiyi tasiri kai tsaye ga rayuwar talakawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: