Mikel Arteta Kochin Arsenal ya Kamu Da coronavirus

0 335

Mahukunta a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal sun tabbatar da cewa mai horas da ƙungiyar Mikel Arteta ya harbu da cutar numfashin nan dake cigaba da addabar ƙasashen Duniya tun bayan ɓullarta daga ƙasar China.

Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Andalus ya bayyanawa shafin ƙungiyar ne na yanar Gizo cewa; “Ban ji daɗin wannan lamari ba amma dai naje ai yi min gwajin cutar tun bayan da na fara jin jiki na yana min wani iri. Zan dawo bakin aiki da zarar an yarjejeniya min.”

Mahukunta ƙungiyar sun sanar da cewa za a killace duk wani ɗan wasa da yayi mu’amala da shi mai horarwas don cigaba a bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: