Fadar Masarautar Birtaniya ta Buckingham ta sanar da mutuwar Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila a yau Juma’a.
Yarima Philip ya mutu ne yana da shekara 99 a duniya.
A wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: “Cikin tsananin jimami Mai martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da mutuwar mijinta abin ƙaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburgh.
“Mai martaba ya mutu a wannan safiyar a Fadar Windsor.”
A watan Maris, aka sallami Duke na Edinburgh daga asibiti bayan da ya shafe wata ɗaya yana jinya.
An yi masa wani ƙaramin aiki ne kan abin da ya shafi zuciya a wani asibitin da ke Landan – St Bartholomew.
Yariman ya auri Gimbiya Izabel ne a shekarar 1947, shekara biyar kafin ta zama Sarauniya, kuma su ne masu mulkin da suka fi daɗewa a kan karaga a tarihin Masarautar Ingila.
Yarima Philip ya mutu ya bar ƴaƴa huɗu da jikoki takwas da kuma ƴaƴan jikoki 10 da suka samu tare da Sauraniyar Ingilan.
An haifi babban ɗansu, Yariman Wales wato Yarima Charles, a shekarar 1948, sai ƙanwarsa Gimbiya Anne a shekarar 1950, sai Duke na York Yarima Andrew a shekarar 1960 sai Yarima Edward a shekarar 1964.
An haifi Yarima Philip a Tsibirin Corfu na Girka a ranar 10 ga watan Yunin 1921.
Mahaifinsa shi ne Yarima Andrew na Girka da Denmark, ƙaramin ɗan Sarki George na I.
Mahaifiyarsa Gimbiya Alice ƴa ce ga ord Louis Mountbatten kuma tattaɓa-kunnin Gimbiya Victoria.
Asalin Labarin: https://www.bbc.com/hausa/labarai-56690568