Me Ƙungiyar Izala ta ce kan matsalolin tsaro a Najeriya?

0 399

Shugaban Kungiyar wa’azin musulunci ta Izalatil Bid’ah, Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, yayi Allah wadai da kisan gilla da kungiyar Boko Haram tayiwa manoman shinkafa ‘yan asalin jihar Sokoto, a kauyen koshobe da ke yankin karamar hukumar Jere a jihar Borno wanda alkaluma suka nuna mutum 46 sun rigamu gidan gaskiya.

Sheikh Bala Lau ya kara jaddada kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi don dakile wannan ta’addanci, don lalle Allah zai tambaye su kan jinin Al’umma dake zuba babu gaira babu dalili.

Shehin Malamin yayi kira na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara daukan kwararan matakai na tsare wannan kasa ta Naijeriya daga dukkan Nau’oi na taadanci da ya addabi kasar

Shugaban na Izala ya karkare da kira ga jama’a da a kara tuba ga Allah Ta’ala, sannan a dukufa da addua a masallatai da makarantu da gidajen mu da sauran wurare na ibada.

Allah ya kawo mana karshen wannan ta’addanci a kasar mu mai Albarka. A cewarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: