MDD ta yi kasa da tutocinta domin nuna juyayi kan mutanen da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza

0 272

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kasa da tutocinta domin nuna juyayi kan mutanen da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza.

Ma’aikata sun yi shiru na kimanin minti daya a daukacin ofisoshin Majalisar Dinkin Duniyar a nahiyar Asiya a safiyar yau Litinin domin tunawa da mamatan.

Majalisar ta tuna da mutanen da aka kashen ne bayan da ta sanar da yawan mutanen da aka kashe a cibiyarta da ke Zirin Gaza.

Hukumar Jinkan Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta  a ranar Juma’a ta sanar da cewa an kashe jami’anta sama da 100 a Gaza, tun bayan fara yakin. Isra’ila na ta yin luguden bama-bamai a fadin yankin Zirin Gaza tun bayan da mayakan Hamas suka kai mata wani kazamin hari a ranar 7 ga watan Oktoba, inda kungiyar ta kashe mutane 1,200 ta yi garkuwa da wasu 240.

Leave a Reply

%d bloggers like this: