MDD ta ce Najeriya na sahun kasashe 3 da za su fuskanci yunwa matsananciya

0 200

Hukumomin abinci na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi gargadin yiwuwar miliyoyin jama’a a kassahen Yemen, Sudan ta Kudu da kuma Arewacin Najeriya su fuskanci matsananciyar yunwa da karancin abinci a watanni kalilan masu zuwa.

Wani rahoto da shirin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP tare da hukumar Noma da Abinci ta Majalisar FAO suka fitar ya nuna cewa al’amura masu alaka da rikice-rikice tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin isar kayakin jinkai, baya ga sauyin yanayi na kan gaba a jerin dalilan da za su haddasa yunwar wadda a cewar kungiyoyin ka iya kai wa ga rasa dimbin rayuka.

Rahoton hadin gwiwar hukumomin abincin biyu, ya nuna cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa a yankunan da suka kunshi, Yemen, Sudan ta kudu da kuma arewacin Najeriya don kaucewa fuskantar bala’o’in da aka yi hasashe nan da watan Yuli mai zuwa.

A cewar rahoton kasashen 3 da ke matsayin na gaba-gaba da za su fuskanci karancin abincin da kuma matsananciyar yunwa da za ta kai ga rasa dubunnan rayuka wani bangare ne na yankuna da kasashe 20 wadanda hukumomin biyu suka gano za a fuskanci matsalar a bana.

Sauran kasashen da za su tsinci kansu a matsalar ta kamfar abinci sun hada da Afghanistan, Burkina Faso, Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo kana Habasha da Haiti sai Honduras da Sudan da Syria da kuma Zimbabwe.

Rahoton ya nuna cewa galibin kassahen yanzu haka wani sashe na su na fuskantar matsalar ta kamfar abinci wanda ke da nasaba da kodai rikicin kabilanci ko kuma hare-haren ta’addanci ko yaki ko kuma matsin tattalin arziki.

Rahoton ya ce a Sudan ta kudu kadai akwai yiwuwar mutane miliyan 7 ad dubu 200 su fuskanci tsananin yunwa sai kuma wasu miliyan 16 da dubu 200 a Yemen kana wasu miliyan 1 da dubu 200 a arewacin Najeriya nan da watan Agusta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: