A jiya ne dai manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka yi Allah wadai da kazamin harin makami mai linzami da Rasha ta kai a birnin Odesa na kasar Ukraine wanda ya lalata wasu gine-ginen tarihi.
A cikin makon da ya gabata, Rasha ta kai hare-hare ta sama kan Odesa da wasu biranen masu tashar jiragen ruwa, tun bayan da ta dakatar da shirin fitar da hatsi da taki zuwa kasashen waje.
Kafofin yada labarai na kasa da kasa sun ruwaito cewa akalla mutum daya ya mutu sannan wasu sama da 20 sun jikkata a harin na jiya.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin tare da nuna damuwa kan yadda yakin ke kara yin barazana ga al’adu na Ukraine. UNESCO ta tabbatar da lalacewar wuraren al’adu 270, ciki har da wuraren addini 116, tun farkon mamayewar Rasha a ranar 24 ga Fabrairu, 2022.