Daruruwan mazauna birnin Derna da ke gabashin Libya a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hukumomin yankin, fiye da mako guda bayan ambaliyar ruwa ta kashe dubban mutane a birnin.
Masu zanga-zangar sun soki shugaban majalisar dokokin gabashin ƙasar, Aguila Saleh, da hukumomin, inda suka dora alhakin ambaliyar da ta kashe kusan mutum 4,000, a cewar alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, masu zanga-zangar sun ce suna son a gaggauta gudanar da bincike kan ambaliyar ruwan da kuma daukar matakin shari’a kan shugabannin da ke da hannu.
Sun kuma buƙaci a biya su diyya da sake gina Derna.
Masana sun kuma bayyana cewa rashin kula da madatsun ruwa na birnin da hukumomi suka yi ne ya sa suka fashe tare da fitar da ruwa.
Masu zanga-zangar sun kuma kona gidan magajin garin Derna, Abdulmenam al-Ghaithi.
Tuni dai Firaministan Libiya Osama Hammad ya dakatar da Mista Ghaithi tare da wasu jami’an karamar hukumar Derna.