Mayakan Boko Haram sama da dubu 8 sun mika wuya ga sojoji a jihar Borno

0 213

Mukaddashin Babban Kwamandan Runduna ta 7, Abdulwahab Eyitayo, ya ce kawo yanzu mayakan Boko Haram sama da dubu 8 sun mika wuya ga sojoji.

Ya ce mayakan sun mika wuya daga maboyarsu a dajin Sambisa, da sauran guraren buyarsu.

Eyitayo, wanda kuma shi ne Kwamandan Sashi na 1 na Operation Hadin Kai, ya bayyana hakan a lokacin da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, da tawagar wakilan tsaro daga Abuja suka kai masa ziyara jiya a Maiduguri.

Ya ce mika wuya da mayakan da suka tuba wani abin farin ciki ne, ya kara da cewa, zafafa yaki da sojojin ke yi ne ya jawo hakan.

Babban Kwamandan ya yi gargadin cewa lokaci zai zo da ba za a sake bude kofa ga mika wuya ba, inda ya bukaci masu tausayawa mayakan da su basu shawarar mika wuya su tuba.

Ya kara da cewa duk wanda ke goyon bayan mayakan shima sojojin kasarnan za su dauke shi a matsayin abokin gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: