Matsalar Kashi A waje, An Kaiwa Jigawa Agaji

0 378

Gwamnatin jihar Jigawa da hadin gwuiwar shashin tallafawa kasashen waje na Birtaniya (DFID) sun gina bandakuna guda 44 a karamar hukumar Birniwa domin magance matsalar yawaitar yin bahaya a waje.

Jami’in dale kula da shirin tsaftar ruwansha na yankin Birniwan, Alhaji Isyaku Umar ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Alhamis.

Umar ya bayyana cewa dukkannin bandakunan an gina su ne a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli kuma an jona musu ruwa daga tankin sama na birtsatsai.

Ya kara da cewa bandakunan an gina su ne a babban asibitin Birniwa da makarantar kimiyya ta yan mata ta gwamnati da makarantar Sakandire ta Sarkin Arewa da Dolen Kwana da Firamaren Matamugu da sauransu.

Jami’in ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitin da za suke lura da su da kuma hada kudi domin gyaransu.

Kana ya ce daga cikin aikisa a matsayin shugaban kwamitin har da tabbatar da ilimantar da mutanen yankin muhimmancin tsaftar ruwan shansu da dabarun gujewa ta’ammali da gurbataccen ruwa a muhallinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: