Shugaban Kungiyar Kwadago (TUC), Festus Osifo, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbacin cewa matatar man Fatakwal za ta fara aiki a karshen shekara.
Osifo, tare da takwaransa, shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, sun gana da Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar jiya yayin wata zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.
Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG), da kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), da kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), da kuma kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sun shiga zanga-zangar. .
Da yake jawabi yayin da ake gabatar da shirin siyasa a gidan Talabijin na Channels shugaban kungiyar ya bayyana cewa zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar ta yi nasara sosai kuma ta yi tasiri wajen zaburar da shugaban kasar wajen gyara manyan matatun mai a fadin kasar.
Shugaban na PENGASSAN ya kuma bayyana cewa kungiyoyin kwadago za su tabbatar da cewa sun yi duk wata mai iyuwa wajen ganin shugaba Tinubu bai yi watsi da maganar zanga zanga ba.