Matatar Dangote ta fara sayar da man fetur kai-tseye ga ‘yan kasuwa

0 130

Matatar man Dangote ta fara sayar da man fetur kai-tseye ga ‘yan kasuwa bayan janyewar dillancin man da babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya yi.

‘Yan kasuwar da dama – waɗanda suka jima suna shigo da man daga ƙetare – sun zaƙu a fara sayar musu da man kai-tseye daga matatar ba tare da wani mai dillanci a tsakiya ba.

A makonnin da suka gabata ne dai babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya sanar da janyewa daga dillancin man na Dangote, domin bai wa ‘yan kasuwar damar sayen man kai-tseye daga matatar.

Ana ganin wannan matakin zai kawo sauki ga matsalar ƙarancin man fetur da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: