Matasa sun kashe wani mutum bisa zargin yin kalamai na ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW) a Ningi jihar Bauchi

0 189

Gungun wasu matasa ya kashe wani mutum mai suna Yunusa bisa zargin yin kalamai na ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW), a ƙaramin ofishin ƴansanda na Nasaru da ke ƙaramar hukumar Ningi a jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3 na rana, shekaran jiya Laraba, lokacin da musu ya ɓarke tsakanin shi Yunussan da kuma wani mutum, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani da aka yi abin a gaban idonsa, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya yi bayanin yadda da farko ƴansanda suka ceci Yunusan lokacin da jama’a suka fara dukan mutumin.

Ya ce, ”ƴansanda sun kai mutumin da ake zargin ƙaramin ofishinsu a cikin garin, amma kuma mutanen sun ci ƙarfinsu, inda suka kashe shi.”

Mutumin ya ƙara bayani da cewa bayan sun kashe Yunusan ne ƙaramin ofishin na Nasaru, sai suka ɗauki gawarsa suka kai ofishin ƴansanda na Ningi.

Rundunar ƴansanda ta jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: