Matakin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi ya haifar da wahalhalu ga ‘yan ƙasar
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce tun asali dama yana da ƙwarin gwiwar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairun da ya gabata, duk kuwa da tsarin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa a ziyara da ya kai wa sarakunan gargajiya na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar nan.
Yayin da yake magana kan matsalolin da ya fuskanta a zaɓen shugaban ƙasar da ya kai shi ga nasara, shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matakin taƙaita yawan kuɗi da batun sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi.
Tinubu ya kuma gode wa sarkin Ijebu bisa shawarar da ya ba shi, game da yadda zai ɓullo wa ƙalubalen a lokacin da ya ziyarci fadarsa a baya.
Ya ce ya yi amfani da ƙwarin gwiwa da sarkin ya nuna masa domin magance ƙalubalen da ya fuskanta a zaɓen. Matakin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ya haifar matsaloli masu tarin yawa da wahalhalu ga ‘yan ƙasar.