- Nisantar cunkoson jama’a da aƙalla tsawon mita guda.
- A goge wuraren taɓawa da hannu da ruwan kashe ƙwayoyin cuta.
- A riƙa wanke hannu aka-akai da ruwa da sabulu, da ruwan sinadarin kashe ƙwayoyin cuta.
- A guji taɓa hanci, baki da ido da hannun da ba a da tabbacin kuɓutarsa daga ƙwayoyin cutar.
- A tare atishawa ko tari da gwiwar hannu maimaikon tarewa da tafin hannu.
Ka sani cewa idan mai cutar COVID-19 yayi tari ko atishawa da hannunsa sannan kuma ya gaisa da wani da hannun, hakan zai iya yaɗa cutar zuwa ga wanda suka gaisa da shi.