Mataimakin Shugaban Kasa yace gwamnatin tarayya tana bisa turbar cimma manufarta ta shekarar 2030

0 217

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yace gwamnatin tarayya tana bisa turbar cimma manufarta ta shekarar 2030 na dorewar cigaba da kiwon lafiya ga kowa da kowa.

Da yake jawabi a Lagos a wajen taron bude wani asibiti mallamkin kamfanin Alpha Mead, Osinbajo yace ta hanyar hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, Najeriya zata cimma manufofin da ta sanya a gaba.

Osinbajo wanda ya samu wakilci a wajen taron daga babban mai taimakawa shugaban kasa akan manufofin dorewar cigaba, Adejoke Orelope.

Yace manufofin dorewar cigaba na majalisar dinkin duniya na kokarin kawo karshen talauci da yunwa da kawar da rashin daidaito tsakanin kasashe, da gina zaman lafiya da adalchi, da sauransu.

Shugaban kamfanin Alpha Mead, Mutiu Sunmonu yace asibitin shine jigo wajen samar da mafita kan kalubalen kiwon lafiya da Najeriya ke fuskantar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: