Mataimakin gwamnan Kano ya jagoranci tawaga zuwa Edo kan kisan matafiya a Uromi

0 81

Wakilan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashi jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo sun tafi jihar Edo domin faɗaɗe bincike tare da tattauna batun kisan matafiya ƴan arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar wadda ke kudancin Najeriya.

Tawagar ta ƙunshi shi mataimakin gwamnan, da Sarkin Rano Ambasada Mohammad Isa Umar da kwamishinonin addini da na ƙananan hukumomi da na ayyuka na musamman da ta harkokin mata da shugaban ƙaramar hukumar Bunkure da sauransu, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Garba Shuaibu ya nuna a wata sanarwa da ya fitar.

Da yake jawabi a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano kafin tafiyarsu, Gwarzo ya ce za su tafi Edo ne domin su yi bincike, “ta hanyar tattaunawa domin gano haƙiƙanin yadda lamarin ya auku domin samar da matsaya mai inganci.”

Ya ce ba wai za su je bincike ba ne kawai, “zuwan zai taimaka wajen ƙara sulhunta tsakanin al’ummomi domin kare sake aukuwar lamarin.”

A baya dai gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya ziyarci Kano domin jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe a jiharsa, inda a lokacin ziyarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci a biya diyyar waɗanda aka kashe ɗin, sannan a yi holen waɗanda aka kama da zargin kisan.

Leave a Reply