Masu yiwa kasa hidima zasu dawo a watan Satumba

0 273

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake bude dukkan sansanonin matasa masu yiwa kasa hidima, inda za a fara basu horo daga ranar 10 ga watan Nuwamban gobe.

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya sanar da haka a wani sako da ya wallafa yau a shafinsa na Twitter.

Idan zaa iya tinawa Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe dukkan sansanonin matasa masu yiwa kasa hidima a fadin kasarnan tun a ranar 18 ga watan Maris, bisa fargabar cutar corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: