Masu sayen kayan abinci su ɓoye ne ke haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayan abinci – FCCPC

0 164

Hukumar kula da hakkin masu sayayya ta kasa, FCCPC ta zargi masu sayen kayan abinci su ɓoye da haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar.

Shugaban hukumar, Tunji Bello ne ya bayyana haka jiya Laraba a wani taron masu ruwa da tsaki a birnin Kano. Ya ƙara da cewa binciken da hukumarsa ta yi, ta gano yadda wasu ‘yan kasuwa ke rububin sayen sabon kayan abinci da aka fara girbewa suna ɓoyewa, lamarin da ya ce yana ƙara ta’azzara ƙarancin abincin a kasuwanni, abin da kuma ya ce shi ke haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayyaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: