Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sallami wasu daga cikin wadanda ke rike da mukaman siyasa a jihar ranar Laraba.
A sanarwar haka da ya saka a shafin sa ta tiwita ranar Laraba din, El-Rufai ya yi musu fatan Alkhairi a duk abinda za su tsunduma yi.
Daga cikin wadanda aka kora akwai mai taimaka wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Mohammed Sani Dattijo, Bala Yunusa Mohammed wanda ke aiki a bangaren majalisar jihar.
Sannan kuma akwai Ben Kure , wanda shine maiba gwamna kan harkokin siyasa.
Gwamna El-Rufai ya ce wanna shine zangon farko na zaftare masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin jihar, zango na biyu na nan tafe.
Idan ba a manta ba gwamna El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta zaftare ma’aikatan jihar saboda ta samu kudin kammala wasu daga cikin manyan ayyukan da yake yi a jihar.
Gwamnan ya ce gwamnati ta gano cewa akwai ma’aikata da dama da basu aikin komai a jihar wanda ma ba sai an yi da su ba kawai suna karbar albashin gwamnatin ne ba tare da ana bukatar su ba.
Ya kara da cewa gwamnati na kashe kudin da take karba daga Abuja akan albashi ne kawai, wanda hakan bai dace ba domin ma’aikata kashi 1 bisa dari na mutanen Kaduna, kuma kudin ba na ma’aikata ba ne kawai, na ‘yan Kaduna ne.
Dalilin haka yasa kungiyar kwadago ta yi zanga-zanga a jihar har na kwana uku, wanda daga baya sai da gwamnatin tarayya ta sa ka baki.