Masu haƙa kaburbura da gyara maƙabarta sun koka kan ƙarancin alawus ɗin da ake ba su na naira 3000 a wata.
Wani mai haƙar kabari a maƙabartar unguwar Tudun Wada da ke Kano, Malam Suleiman Mohammed ya shaida wa BBC cewa a wasu lokutan akan biya su ƙasa da naira dubu uku, yayin da mafi yawan alawus ɗin da aka ba su a shekarun baya bai wuce naira 5,000 ba.
Mutumin wanda ya kwashe shekara sama da 30 yana aikin haƙa kaburbura a maƙabartar, ya ce sun kai kukansu gaban Sarkin Kano don nema a ƙara musu alawus-alawus, inda aka yi musu alƙawarin za a duba.
Ya ce tun da fari ana biyan su naira 1,000 ne kacal, kafin a yi musu ƙarin ya kai 5,000 kuma a halin yanzu ya koma naira 3,000 ko 2,500.
A cewarsa wani lokacin akan ɗauki watanni ba a ba su alawus ɗin ba.
“Aikin haƙa kabari abu ne mai wuya,” in ji malam Suleiman “saboda hatsarin da ke tattare da hakan, kuma aiki ne na ƙarfi da ke sanya ciwon jiki, don haka ko nawa za a biya su ba zai yi yawa ba.”
Mai haƙar kabarin ya koka kan yadda wasu ɓata gari ke amfani da maƙabartar wajen adana makamai ko shaye-shaye, lamarin da kan janyo gobara a maƙabartar.
Yayin da a wasu lokutan wasu kan je maƙabartar domin yin abubuwan da suka shafi tsubbace-tsubbace.
Ya nemi a inganta ayyukansu ta hanyar tsaftace maƙabartar da gyara katangarta da sanya fitulu.
Ana amfani da maƙabartar wajen binne mamata daga kimanin unguwanni goma, lamarin da ya sa a yanzu ta cika, sai an lalubo tsohon kabari kafin a binne sabuwar kushewa.