Masarautar Katsina Tabi Sahun Jigawa, Kano Wajen Dakatar Da Hawan Sallah

0 237

Masarautar jihar Katsina, tabi sahun takwarorinta na Kano da nan Jigawa, biyo bayan daukar matakin soke gudanar da shagulgulan bikin sallah babba dake tafe.

Masarautar dai ta aikewa da gwamnatin jihar, dangane da matakin, wanda ta bayyana matsalar tsaro, hadi da cutar alakakai ta corona, a matsayin musabbabi.

Wasikar wadda aka rubuta da yaren Hausa, aka kuma aikewa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Inuwa Mohammad, na dauke ne da sa hannun sakataren masarautar kuma sallaman Katsina Alhaji Mamman Ifo.

Cikin wasikar, masarautar ta bukaci al’umma da gudanar da bukukuwan sallarsu daga gida, tare da rokon su da suyi amfani da lokacin, wajen yiwa jihar dama kasa baki daya Addua.

Leave a Reply

%d bloggers like this: