Masarautar Hadejia ta mika sakon jaje da ta’aziyyarta ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon matsalar tsaro

0 200

Majalisar Masarautar Hadejia ta mika sakon jaje da ta’aziyyarta ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon matsalar tsaro da ta haifar kashe-kashen gilla a yan kwanakin nan.

Da yake jawabi a wani taron hadin guiwa da al’umomin yankin da abin ya faru Galadiman Hadejia, Alhaji Usman Abdul’aziz.

Yayi Addur Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya baiwa yan uwa hakuri da juriya. Taron dai na da nufin tattauna hanyoyin da za a bi don kawo karshen matsalar tsaron, inda ya jaddada cewa harkar tsaro aiki ne na hadin gwiwa tsakanin al’umma, jami’an tsaro da mahukunta.

Sannan yayi kira ga shugabannin gargajiya, iyaye da duk masu ruwa da tsaki da su hada kai domin kawo mafita. Kazalika, Alhaji Usman Abdul’aziz ya tunatar da Hakimai da su sake kafa kwamitin dattijai mai mutane ‘goma-goma’ a kowanne yanki don lura da harkokin tsaro da ci gaban yankunansu.

Tun da farko, Hakimin Waje, Katukan Hadejia, Alhaji Iliyasu Ibrahim, ya gabatar da shugabannin yankunan da suka hada, dagatai da ‘yan kwamitin dattijai daga unguwannin NTA, Shagari, Warwarin, Bello Bayi da kuma Mandara.

Leave a Reply