Masar, Habasha, Iran, Saudiya da Dubai zasu zama cikakkun Mambobin BRICS

0 430

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa a jiya ya sanar da cewa kungiyar kasashe masu tasowa ta BRICS ta sanya kasahen Saudiya, hadaddiyar daular larabawa da kuma Iran cikin Mambobinta.

Shugaba Cyril Ramaphosa a ya fadi haka ne a taron shugabannin kungiyar wanda aka yi Johannesburg babban birnin kasar,inda yace kasar Masar, Habasha, Iran saudiya da Dubai zasu zama cikakkun Mambobin BRICS.

Kasashen Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu -sune suka mamaye ajandar taron a taron na kwanaki uku da suka yi tare dan bayyana irin rarrabuwar kawuna a tsakanin kungiyar dangane da saurin da ka’idojin karbar sabbin mambobi.

Shugaba Cyril Ramaphosa yace kungiyar, wacce ke yanke shawara bisa yarjejeniya, ta amince da ka’idoji, da hanyoyin aiwatar da tsarin fadada BRICS.

Akalla kusan kasashe 12 ne suka nemi shiga kungiyar a hukumce, wanda ke wakiltar kashi ɗaya bisa huɗu na tattalin arzikin duniya da fiye da mutane biliyan uku.

Wasu daga cikin shugabannin kasashe 50 sun halarci taron wanda ya gudana Johannesburg,wanda ya kare a wannan alhamis din.

Leave a Reply

%d bloggers like this: