Manyan kifaye sun kashe masu ninƙaya, ‘yan Rasha biyu a tekun Philippines

0 23

Wasu masu ninƙaya biyu ‘yan ƙasar Rasha sun mutu a Philippines, inda aka ƙwato gawar ɗaya daga cikinsu daga tarin wasu manyan kifaye na shak da ke cin gawarsa.

Mutanen biyu na tare ne da wasu ‘yan yawon buɗe idanu biyu da kuma jagoransu inda suka je ninƙaya a ɗan ƙaramin tsibirin Verde.

Igiyar ruwa mai ƙarfi ce ta raba mutanen a lokacin da suke ninƙaya. Ruawa ya ci ɗaya daga cikin mutanen, yayin da ɗayan aka same shi a tsakanin manyan kifayen na shak suna cin jikinsa.

Sun cicci hannun mutumin ɗaya. Ba a sani ba ko ya mutu ne kafin ko kuma bayan sun kaimasa hari.

Leave a Reply