Majalisar malamai ta jihar Kano a yau ta sanar da dakatar da fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ibrahim Khalil, daga matsayin shugabanta.
An maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban riko.
Majalisar ta zargi Sheikh Ibrahim Khalil da siyasantar da lamurran majalisar tare da amfani da ita don biyan bukatun kansa.
Malaman, daga manyan mazhabobi uku na Tijjaniyyah da Kadiriyya da Izala, sun sanar da matsayin a wani taron manema labarai a Kano.
Har ya zuwa nadinsa, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan shine Shugaban Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa’ikamatus Sunnah na Jihar Kano.