Manyan ƴan adawa a Najeriya sun yi fatali da dokar ta-ɓaci a Rivers

0 67

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai da ɗantakarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour, Peter Obi sun yi fatali da matakin Shugaban Najeria na ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar Rivers.

El Rufai da sauran jagororin jam’iyyun hamayya sun buƙaci Majalisar dokokin Najeriya ta yi watsi da ƙudirin.

A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Siiminalayi Fubara da mataimakiyarsa da mambobin majalisar dokokin jihar.

Shi ma ɗantakarar shugaban ƙasa a 2023 ƙarkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, a jawabin a ya yi ranar Alhamis, ya zargi Tinubu da nuna ɓangaranci.

Atiku Abubakar ya kuma nemi Shugaba Tinubu da ya janye matakin wanda ba ya bisa kundin tsarin mulkin ƙasa sannan ya maido da zaɓaɓɓn gwamna da mataimakiyarsa da sauran mutanen da aka dakatar kan kujerarsu.

A cewarsa sun yi tur da matakin sannan sun yi kira ga ƴan Najeriya da su soki ƙudirin wanda ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma dimokraɗiyya.

  • Mece ce dokar ta-ɓaci kuma me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce a kan ta?
  • Me ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ke nufi?

– BBC Hausa

Leave a Reply