Manufarmu ita ce samar da tsarin kiwon lafiya na zamani wanda zai biya bukatun jama’a – DLD

0 134

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an yi ayyukan da suke da matukar muhimmanci.

Dauda Lawal ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake kaddamar da babban asibitin da aka gyara a karamar hukumar Maru.Hakan na zuwa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris ya fitar jiya.Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnatin Lawal na shirin gyarawa da kuma samar da kayan aiki ga daukacin manyan asibitocin jihar.

Ya kara da cewa, a yayin da yake duba kayayyakin more rayuwa da na’urorin kiwon lafiya da aka samar a babban asibitin Maru, Gwamnan, ya bayyana cewa manufarsa ita ce samar da tsarin kiwon lafiya na zamani wanda zai biya bukatun jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: