Kungiyar dukkan manoman Najeriya, AFAN, ta roki gwamnatin tarayya da ta bayar da diyya ga manoma bisa asarar da suka tafka yayin aiwatar da kudirin fasalin kudi na babban bankin kasa CBN da kuma karancin takardun kudi.
Manoman sun yi rokon yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa yau a Lagos, lokacin da suke bibiyar illar kudirin akan samar da kayan abinci da kasuwancin gona.
Sun ce akwai bukatar bayar da diyyar domin karfafawa manoma gwiwar komawa gona.
Manoman sunce ya kamata a bayar da diyyar ta hanyar raba kudade, iri, taki da kuma kayan aikin gona.
Sun kara da cewa hakan zai basu damar cimma kudirin da aka sanya a gaba ta samar da abinci a bana.
Shugaban kungiyar na shiyyar Lagos da yankin Kudu maso Yamma, Dr. Femi Oke, yace aiwatar da kudirin ya shafi ‘ya’yan kungiyar da yawa, lamarin da ya kawo tsaiko a harkokin noma.
A cewar Femi Oke, kudirin hada-hada ba tare da takardun kudi ba da na sake fasalin takardun kudin sun shafi manoma sosai.
- Comments
- Facebook Comments