Maniyyata Hajji su fara ajiye naira miliyan 8.5 a jihar Legas

0 183

Hukumar Jin Daɗin Alhazan jihar Legas ta buƙaci maniyyata a jihar da su fara ajiye naira miliyan 8.5 domin Hajjin shekarar 2025.

Hukumar ta buƙaci dukkan maniyatan da suke da niyyar zuwa Hajjin na baɗi su cire fom ɗin fara biyan kuɗin daga shafinta na intanet.

Babban Sakataren hukumar, Mista Saheed Onipede ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin hukumar Mista Taofeel Lawal ya fitar a ranar Laraba.

A cewar Onipede, kuɗin fom ɗin Naira 20,000 ne, sannan maniyyata za su fara ajiye Naira 8,500,000.00, kafin Hukumar Hajji ta Ƙasa wato NAHCON ta ayyana asalin kuɗin kujerar Hajjin.

Har yanzu dai ana tsimayin kuɗin kujerar Hajjin na baɗi a daidai lokacin da jihohi suka fara bayyana ƙudin ajiya da za a fara biya kamar yadda Daily Trust ta bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: