Manhajojin lamuni dake kan manhajar Play Store za su rasa ikon samun damar bayanan masu amfani da su daga ranar 31 ga watan Mayu.
Wannan ya zo ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta aiwatar da sabuwar manufar Google, tana mai cewa matakin ya yi daidai da matakin da hukumomin Najeriya suka dauka na dakile mamaye bayanan sirrin kwastomomi da kamfanonin hada-hadar kudi ke yi.
A cikin ‘yan kwanakin nan gwamnatin tarayya ta dauki manyan matakai da nufin magance keta sirrin kwastomomi ta hanyar amfani da manhajojin waya.
Musamman ma, Hukumar Kula da Kasa ta Tarayya da Hukumar Kare hakin mai saye a kwanan nan ta yi wa manhajoji 170 rajista daga cikin 200 da ke aiki a kasar.
Wannan sabuwar dokar da zata fara aiki na zuwa ne bayan kamfanin ya sanar da sabunta Shirin Haɓaka shirye-shiryen ta, wanda ya tilasta masu ba da lamuni na dijital a Najeriya, Indiya, Indonesiya, Philippines, da Kenya su bi ka’idodin tsari ko kuma a dakatar da su zuwa ranar 31 ga Janairu.
- Comments
- Facebook Comments