Malam El-Zakzaky ya gana da wadanda suka tsira daga rikicin 2015 da sojoji Najeriya

0 238

Jagoran Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi ta Shi’a a kasarnan, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya gana da wadanda suka tsira daga rikicin watan Disambar 2015 tsakanin sojoji da ‘yan kungiyar.

Sheikh Zakzaky ya kuma gana da iyalan wadanda aka kashe a rikicin.

Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar 28 ga Yuli, 2021, ta sallami tare da wanke Sheikh da matarsa, Zeenat wadanda aka gurfanar a gabanta kan tuhume-tuhume takwas da ke da alaka da zargin hada baki da laifin kisan kai.

Sai dai a lokacin da yake jawabi a Abuja, Shehin Malamin ya yi amfani da wannan dama ya jajanta musu kan asarar ‘yan uwansu da suka yi.

Ya yi ishara ga masu ziyartar sa cewa babu sadaukarwa da take yawa a aikin Allah.

Har ila yau Shaikh Zakzaky ya nemi gafara bisa gayyato wasu daga cikinsu, maimakon ya je gidajensu don yi musu ta’aziyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: