Mako guda ya rage a rufe shafin daukar sababbin ‘Yansanda a fadin Najeriya

0 286

Hukumar ‘Yansanda ta fitar da sanarwar cewa mako guda ya rage kafin ta rufe shafin daukar sababbin ‘Yansanda a fadin kasar nan.

Yanzu haka dai shafin ya samu masu neman aiki kimanin mutum dubu 547 da dari 774 a matsayin masu neman aiki Dan sanda a rundunar ‘yan sandan gabanin rufe shafin a ranar Lahadi mai zuwa, wanda zai cika makonni 6 na wa’adin da hukumar ta sanya.

An buɗe shafin a ranar 15 ga Oktoba, 2023, makonni biyar da suka gabata.

Daga cikin dubu 547 da  dari 774 masu neman aiki, dubu 358 da dari 900 sun yi nasara kuma sun cancanci zuwa zagaye na gaba na tsarin daukar ma’aikata wanda ya hada da yanayin kirar jikinsu da lafiyarsu da ingancin takaddunsu bayanansu.

An cire akalla mutane sama da dubu 84 da dari 606 na masu neman aikin wadanda shekarunsu na haihuwa suke tsakanin shekaru 18 zuwa 25, inda aka fitar da su. Jihar Kaduna ce Jiha ta farko a matsayin jihar da ta fi kowacce yawan masu nema aikin da Mutum dubu 40 da dari 272 sai Jhar Anambra wadda take a matsayin Jiha ta karshe da Mutum dubu 16,64.

Leave a Reply

%d bloggers like this: