Majalissar zartarwa ta jihar kano ta umarci a dauki malaman makaranta 5000

0 247

Majalissar zartarwa ta jihar kano, ta umarci shugaban ma’aikatan jihar da ya dauki malaman makaranta masu shedar takardar koyarwa kimanin 5,000.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba, shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishin sa.

Yace biyo bayan matsalar ilimi da jihar ke fuskanta, kwamitin ilimi yayi duba akan hakan da kuma fitar da tsarin ilimi kyauta a jihar.

Kwamishinan jihar, ya kara da cewa bayan nazartar sakamakon da kwamitin ilimi ya fitar ta ofishin sakatarn gwamnatin jihar, sun amince a dauki wadanda sukayi Digiri a fannin koyarwa, da ma masu karatun NCE da Diploma.

Mallam Muhammad Garba ya ce, ma’aikatan da suke aiki a ma’aikatar ilimi, hukumomi, da kananan hukumomi, za’a aika musu da kayan aikin da suke bukata ciki harda makarantun gaba da sakandire.

Leave a Reply

%d bloggers like this: