Kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar dattawa ya tuhumi wasu ma’aikatu da hukumomi 558, kan gazawa wajen bada cikakken bayani na kudi kimanin Naira Bilyan 969 na kadarorin gwamnati a kundin kasafin kudi na shekarar 2019.
Yan majalisar, yayin da suka yin Nazari kan rahotan na babban mai bincike na gwamnatin tarayya, ya nuna yadda ma’aikatu da hukumomi suka gaza tabbatar da yawan kadarorin.
Mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia yace wannan rahotan na cikin bayanan babban mai bincike ba gwamnatin tarayya.Babban akawunta na kasa yace za’a yi gyara a kadarorin gwamnatin domin yayi dai-dai dana shekaru masu zuwa.
Daga cikin hukumomin akwai hukumar kula da kadarorin gwamnati ta kasa, da hukumar harkokin sayer da kadarorin gwamnati,da kwalen Gandun daji ta gwamnatin tarayya dake ibadan,sai kuma hukumar wayar da kan jama’a,da kwalejin horas da yan sanda ta WudilSauran hukumomin sun hada da hukumar tattara haraji, ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro,ma’aikatar harkokin cikin gida,hukumar shige da fice ta kasa da hukumar kashe gobara, hukumar tsraon farin kaya ta civil defence, sai kuma ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa,hukumar bada rancen gidaje,da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki sai kuma hukumar kula da kafafen yada labarai.