Majalisar Wakilan Najeriya ta fara binciken zargin USAID da taimaka wa ‘yan ta’adda a kasar

0 90

Majalisar Wakilan ta fara binciken kudaden da wasu kungiyoyin agaji ke sarrafawa bayan da wani dan majalisar dokoki na Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar USAID da taimaka wa ‘yan ta’adda a kasar nan.

A wata wasika da aka aikawa kungiyoyin a ranar 10 ga watan Maris din nan, majalisar ta bukaci bayanan hada-hadar kudade daga shekarar 2015 zuwa 2024, tare da cikakkun bayanai kan kudaden shigarsu da fitarsu da kuma bayanan masu duba asusun su.

Sai dai wasu daga cikin kungiyoyin sun ce majalisar ba ta da ikon bincikar su, inda kungiyar CISLAC ta bukaci kwamitin da ya mai da hankali kan hukumomin da ke karkashin ikon majalisar.

Zargin Scott Perry ya haddasa tunzuri a yankin Arewa, inda rikicin Boko Haram ke haddasa matsalar jin kai, amma jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya musanta duk wata alaka tsakanin USAID da ‘yan ta’adda, yana mai cewa akwai tsauraran matakai na tabbatar da cewa ba a karkatar da kudaden ga kungiyoyin ta’addanci ba.

Leave a Reply