Majalisar wakilai ta soki jinginar da yancin Nijeriya a yarjejeniyar bashin da China

0 183

Majalisar wakilai ta kasa ta soki batun jinginar da yancin kan kasa a yarjejeniyar bashin Najeriya da China, inda tace abune mai hadari sosai.

Shugaban kwamitin yarjejeniyoyi na majalisar, Nicholas Ossai, wanda ya sanar da haka a Abuja, a wajen taron jin bahasin basussukan kasashen waje, yace yarjejeniyar bashin Najeriya da kasar China, tana aiki ne da dokokin kasar China.

Yace duk da kasancewar gwanatin tarayya a shekarar 2014, ta sanya hannu akan dokar majalisar zartarwa wacce ta samar da ka’idoji akan jinginar da yancin kan kasa lokacin tattaunawar yarjejeniyar, jami’an gwamnatin tarayya na taka dokar.

Mambobin majalisar zartarwa wadanda suka bayyana a gaban kwamitin sun hada da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, da ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami, da ministan harkokin yansanda, Muhammad Maigari, da ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: